Kasar sudan ta fada wani yajin aikin kwana biyu daga yau talata a wani mataki na neman sojojin kasar su kafa gwamnati kamar yadda masu fafutaka suka bukata.
Tun farkon wannan watan ne dai sojojin kasar Sudan sukayi nasarar hanbare gwamnatin Umar Bashar Albishir na sudan a wani mataki na neman sauyin shugabancin kasar.
Bayan hanbarar da gwamnatin Albashir wasu masu fafutuka a kasar suketa fafutukar ganin an kafa gwamnatin farar hula wanda har yanzu baiyi nasara ba, wanda daga baya a Yau din-nan suka tsunduma yajin aiki don samun abunda suke nema na kafa Gwamnatin farar hula a kasar.