Ministan masana’antu da kasuwanci Okechukwu Enelema yace Gwamnatin tarayya zata samar da ayyukan yi milyan 20 a bangaren noma, gine-gine, Sufuri, da kuma sauran abubuwa a mulkin su cikin Zango na biyu.
Ministan ya fadi haka ne ranar litinin dinnan a Abuja yayin wani taro da masu ruwa da tsaki kan hanyoyin Samar da aikin yi na Gwamnatin tarayya.
Ministan Wanda ya samu wakilcin Sunday Akpan Wanda shine sakataren din din din a ma’aikatar, kamar yadda yace hukumar kula da sanin makamar aiki ta (ITF) ta ba hukumar dama kan kawo tsare tsaren da suka dace ta yadda za a samu Arziki mai Dorewa.
ITF, dai ita ce zata kawo wannan a zangon Malkin na biyu mai taken next level a bangarori Hudu yadda Najeriya zata samu karauwar tattalin arziki inda ya ja hankalin masu ruwa da tsaki kan su bada tasu gudummawa sosai ta yadda za a samu wadannan kudurai su tabbata.
Daraktan ITF Mista Joseph Ari, Yace yawan Kididdigan ‘Yan Najeriya marasa aikin yi na damun Gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari, Kwarai da Gaske.
Yace hukumar kididdiga ta NBS ta ce, yawan marasa aikin ya karu da 17.6 A daya bisa hudun shekara ta 2017 zuwa 20.6 a daya bisa ukun shekarar bara.