By Abbas Yakubu Yaura
Ministan ma’adinai da karafa, Olamilekan Adegbite, ya bayyana cewa ofishin ma’adinai na Cadastre ya inganta kudaden shigar da yake samu daga lasisin hakar ma’adinai daga Nsira biliyan 2.3 a shekarar 2020 zuwa Naira biliyan 3.88 izuwa ranar 31 ga Oktoba na shekarar 2021, inda ya kara da cewa an soke lasisin kusan 1,566 a tsawon wannan lokaci.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a taron makon ma’adinai na Najeriya karo na biyar a ranar Talata.A cewar ministan, ofishin ma’adinai na Cadastre ya inganta tsarin mallakar ma’adinai da kuma gudanarwa.
Sannan yace, “An mayar da ofishin ma’adinan Cadastre don inganta gaskiya da kuma kula da take hakkin ma’adinai.
“An tsara hanyoyin ne domin baiwa masu zuba jari damar yin amfani da yanar gizo da kuma samun lasisi da haya a ciki da wajen Najeriya. Har ila yau, muna kafa ofisoshin MCO a yankuna shida na siyasa. Sun hada da Jos, Enugu, Ibadan, Kaduna, Maiduguri, da kuma Benin.
“Daga hangen nesa na samun kudaden shiga, MCO ya nuna ingantaccen ci gaban da aka samu duk da kalubalen annobar cutar Da ake fuskanta.
Kazalika ” hakan ya bunkasa kudaden shigarta daga Naira biliyan 2.3 a shekarar 2020 zuwa Naira biliyan 3.88 a shekarar 2021 zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, yayin da ya rage saura watanni biyu a wannan shekarar domin samun karin kudaden shiga.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa hukumar ta bayar da rahoto na musamman a watan Satumba cewa an soke lasisin hakar ma’adanai kusan 5,793 a cikin shekaru shida.
Comments 1