Wata kotun majistare da ke zamanta a Wuse, babban birnin tarayya Abuja, ta tasa keyar Farfesa Zainab Duke Abiola zuwa gidan yari na Suleja bisa laifin cin zarafin sufeto Teju Moses, da ‘yan sanda suka kai karar ta.
An gurfanar da Farfesan ce tare da mai taimaka mata a gida, Rebecca Enechido, ranar Juma’ar nan.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, acikin wani faifan bidiyo da ya bazu a ranar Laraba, an ga jami’ar a zaune a kasa tana neman a kai ta asibiti domin a kula da lafiyarta yayin da take zubar jini.
Rundunar ‘yan sandan ta zargi Abiola, wata malamar shari’a kuma mai fafutukar kare hakkin bil’adama, da yunkurin aikata laifin kisa da kuma cin mutunci da gangan.
KARANTA KUMA: Farfesa Ta Musanta Zargin Cin Zarafin Jami’ar Yar sanda
A zaman kotun ranar Juma’ar nan, an hana Farfesan beli yayin da aka dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Oktoba, 2022.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Alkalin kotun ya kuma bayar da umarnin a ci gaba da tsare ta a gidan yari na Suleja har zuwa lokacin da za a sake zaman.
A wani labarin kuma: Daga Karshe Dai Gwamna Wike Ya Ruguza Jam’iyyar PDP – Fani-Kayode
Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, kuma jigo a masu goyan bayan, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC Bola Tinubu,
ya ce gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ruguza jam’iyyar adawa ta PDP.
Lauyan kare hakkin dan Adam ya bayyana haka ne ta hanyar wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta a lokacin da yake mayar da martani ga ficewar Wike a kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.