An tsaurara matakan tsaro a cibiyar samar da wutar lantarki ta gaggawa ta Maiduguri (MEPP) a Borno gabanin kaddamar da aikin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi.
Jaridad DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa a ranar Alhamis shugaban kasar zai kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 50 da gwamnatin tarayya ta gina ta hannun kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Borno.
Maiduguri, wani babban birni a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, ya fada cikin duhu sakamakon barna da hare-haren da ‘yan tada kayar baya suka kai kan muhimman kayayyakin samar da wutar lantarki a garin, lamarin da ya janyo katsewar wutar lantarki.
KARANTA HAKANAN Buhari Ya Isa Maiduguri Kaddamar Da Wasu Ayyukan gwamnati
Abubuwa biyu da suka faru na irin wadannan munanan hare-hare sun hada da lalata hasumiyoyi uku na layukan wutar lantarki a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri da ‘yan ta’adda suka yi a ranar 25 ga watan Janairu da 27 ga watan Maris na 2021.
Shugaba Buhari a watan Afrilun 2021, ya umarci mahukuntan kamfanin na NNPC, da su maido da wutar lantarki a Maiduguri da kewaye.
Bayan tattaunawa da gwamnatin Borno, hukumar NNPCPL ta fara aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 50 da nufin samar da ingantaccen wutar lantarki mai dorewa ga birnin da kewaye.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa an baza jami’an hukumomin tsaron Najeriya da dama da suka hada da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), sojoji da ‘yan sanda a wurin.
Wasu jami’an soji da suka hada da hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC), hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) da hukumar kashe gobara ta tarayya ma suna can a filin.
Haka kuma an ga jami’an hukumar ta NNPC, da ‘yan majalisar ministoci, da wasu iyayen Kasa masu sarauta da wasu kungiyoyin likitoci da kayan aikinsu a wurin.
Ana sa ran shugaban zai samu rakiyar Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu, da takwaransa na albarkatun mai, Cif Timipre Sylva, Gwamna Babagana Zulum da Shugaban Kamfanin na NNPC, Malam Mele Kyari.
Sauran manyan jami’an gwamnati daga gwamnatocin tarayya da na jihohi su ma sun halarci taron. (NAN)
A Wani Labarin Kuma NGOs Sun Bukaci Jam’iyyu Su Kalubalanci Sakamakon Zabe A Kotu, Ba Rikici Ba
Gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu, da suka hardar da Sir Ahamadu Youths Council of Nigeria, da Arewa Youth Council and Arewa Youth Advocates For Good leadership sun bukaci jam’iyyun siyasa da su bi tsarin da ya dace na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na 2023, kada su tayar da rikici.
Kungiyoyin sun yi wannan kiran ne a ranar Laraba ta bakin shugabanninsu, Bilal Tijjani Paki, Zayyad Ayuba Alhaji da Ibrahim Munir Kankara, a wani taron manema labarai a Kano.