Jihar Kebbi ta kori wasu hakiman gundumomi 3 saboda Zargin zamba
Gwamnatin Jihar Kebbi ta tsige hakimai uku na kananan hukumomi uku a masarautar Gwandu bisa laifin zamba da wasu laifukan, da kuma barin Masarautar su ba tare da izini ba.
Da yake sanar da korar da aka yi a Birnin Kebbi a ranar Alhamis, Shugaban Hukumar Kula da Ma’aikatan Jihar Mansur Shehu ya shaida wa manema labarai cewa matakin ya yi daidai da dokar ma’aikata (PSR) na Jihar.
Waɗanda aka sauke sune Lawal Yakubu wanda shi ne na Arewan Yeldu a ƙaramar Hukumar Arewa; da
Ahmed Sani wanda shi ne Sarkin Gabas Geza a ƙaramar Hukumar Dandi da Tukur Aliyu ɗan Jagwadejin Bakuwe a ƙaramar Hukumar Suru.
Shehu ya ce korar hakiman ya zama tilas ne bayan da hukumarsa ta binciki tuhume-tuhumen da ake yiwa kananan hukumominsu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Najeriya za ta yi zama kan sabon mafi ƙarancin albashi a watan Maris – Minista
Hukumar tana da alhakin ladabtar da Ma’aikatan kananan hukumomi daga mataki na 07 zuwa sama (shugabannin gundumomi) kamar yadda dokar kananan hukumomin Jihar Kebbi (2008) ta tanada.
“Bayan samun tuhume-tuhumen, hukumar ta dakatar da hakiman gundumomi tare da kafa kwamitoci da za su binciki zargin da ake musu’’ Mista Shehu ya ce.
Ya bayyana cewa kwamitocin sun kai ziyara tare da tattaunawa da shuwagabannin kansilolin da hakiman gundumomin suke kafin su samu wanda ake tuhuma da laifi kamar yadda ake tuhuma.
An tuhumi waɗannan hakiman da laifin rashin bin ƙa’ida da zamba, da barin Masarautun su ba tare da izini ba.
“Domin tabbatar da kwararan dalilai da hujjoji da kwamitocin suka gabatar, hukumar ta mika batun ga babban lauyan Gwamnati da kwamishinan shari’a domin jin ta bakinsu’’ inji shi.
Ya bayyana cewa babban lauyan ya lura da kowanne daga cikin shari’o’i uku da aka shumigar a hukumance, wanda ya kai ga ci gaba da bincike tare da gano wasu karin shaidun.
Shehu ya ce bayan bincike da tuntuba, hukumar ta samu hakiman da laifin rashin da’a da kuma laifin zamba, wanda hakan ya tilasta korarsu daga Kujerun su na Hakiman ƙananan hukumomin.