By Abbas Yakubu Yaura
Sama da ‘yan kasuwa 70 ne ake fargabar an yi garkuwa dasu a ranar Laraba a lokacin da wasu ‘yan bindiga da suka addabi yankin Birnin Gwari suka kai hari kan ayarin motocin ‘yan kasuwa a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.
A cewar wata majiya, ayarin motocin sama da 20 tare da rakiyar ‘yan sanda na jigilar ‘yan kasuwa ne daga kauyukan karamar hukumar Birnin Gwari zuwa Kaduna da Kano, inda ‘yan bindigar suka far musu.
Ko da yake, rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba ta bayar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, amma kakakin rundunar, ASP Muhammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai ya kasa bayar da cikakken bayani kan adadin wadanda aka sace, inda ya yi niyyar bayar da cikakkun bayanai game da harin lokacin da ya isa ofishinsa.
Majiyoyi sun ce harin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Laraba, inda aka sace mutanen amma ba a samu asarar rai ba, domin daga baya wasu ‘yan kasuwar sun tsere daga harin, duk da cewa yawancinsu basu yi sa’ar tsira ba.
Wani shugaban al’ummar Udawa, Alhaji Muhammadu Umaru, ya shaida wa manema labarai cewa, wasu makwabtan sa hudu na daga cikin wadanda ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su.
A cewar Muhammadu, “Harin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safe a tsakanin Udawa da Buruku dake kan hanyar. An sace hudu daga cikin makwabtana. ’Yan kasuwa ne a kan hanyarsu ta zuwa Kaduna da Kano.inda yace Suna cikin ayarin motoci kusan 30 ne karkashin jagorancin ’yan sanda.
“A cikin ayarin motocin, muna da ‘yan kasuwarmu kusan 70 daga garin Udawa kadai, akwai kuma wasu daga garuruwan da ke makwabtaka da su da harin ya rutsa dasu.
Wata majiya ta shaida wa jaridar Dimokuradiyya cewa sama da matafiya 70 ‘yan fashin suka yi awon gaba dasu cikin daji.