Girgizar kasa ta auku da matakin 5.0 a yankin Hokkaido dake kasar Japan kamar yadda hukumar kula da yanayi ta kasar ta tabbatar a ranar Laraba.
Haka zalika, a Manila dake kasar Philippines girgizar kasar ta auku da karfinta ya kai 6.3 a ranar Laraba kamar yadda cibiyar lura da yanayi na kasar ya tabbatar.
Sai dai ya zuwa hada wannan rahoton, babu tabbacin ko akwai wanda ya raunata ko rasa rai sakamakon girgizar kasar.