Wani mutum mai suna Dogo Shettuma a shafin Twitter yayi martani kan hoton wani mutum yana kallon ƙwallon ƙafa yayin da ake huɗuba a masallaci.
A wani rubutu da ya sanya a shafin nasa na Twitter a ranar 18 ga watan Janairun 2023, Dogo Shettima yace wannan ba halayya bace mai kyau mutum ya riƙa yin irin wannan aikin yayin da ake magana kan koyarwar manzon Allah (SAW). Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Soyayya daɗi: Yadda wani matashi ya sanya aka yanka hannun sa domin rubuta sunan masoyiyar sa.
Mutumin bai jidaɗin wannan ɗabi’ar da mai kallon ƙwallon yayi ba, sannan ya shawarci iyaye da su mayar da hankulan su kan tarbiyyar ƴaƴan su, ba ƙyale-ƙyalen duniya ba, domin a rage aukuwar irin waɗannan halayen waɗanda basu kamata ba.
A cikin masallaci lokacin da liman yake wa’azi da huɗuba kan koyarwar annabi Muhammad (SAW). Yakamata mu mayar da hankali kan tarbiyyar ƴaƴanmu ba ƙyale-ƙyalen duniya ba. A cewar sa
Wannan rubutun na sa ya ɗauki hankula sosao inda mutane da dama suka yi Allah wadai da wannan halayyar da mai kallon ƙwallon ana huɗuba ya nuna. Sun bayyana lamarin a matsayin abin takaici da baƙin ciki.
Bashin N22.7trn: Majalissar Dattawa Ta Bai wa Gwamnan CBN, Da Ministar Kudi Wa’adin Kare Kansu
A wani labarin na daban kuma majalisar dattawa ta ba gwamnan CBN da ministan kuɗi wa’adin lokacin da za su kare kan su kan ɗumbin bashin da aka ciyo.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya baiwa gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele da ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed wa’adin kwanaki uku da su bayar da cikakkun bayanai kan bashin Naira tiriliyan 23.7 da sake fasalin bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a bara.
Majalisar Dattawa ta yi zargin cewa Shugaban kasa da Gwamnan CBN sun saba wa Kundin Tsarin Mulki.