Wani sabon bincike da Kenya National Bureau of Statistics (KNBS) ta saki ya nuna cewa kowanne namiji a kasar Kenya yana lalata da akalla mata 7 a tsawon rayuwarsa, mata kuma maza biyu, LIB ta ruwaito.
KU KARANTA: Boka ya mutu yana tsaka da baje kolin lalata da matar fasto a otal
Kamar yadda rahoton mai taken “Kididdigar Yanayi da Lafiya”, ya nuna, kaso 35 na maza cikin watanni 12 akalla suna saduwa da matan da ba matansu ba kuma ba ‘yan matansu ba idan aka hada da kaso 19 na mata.
Kamar yadda ya nuna:
“An samu rahoton karuwar kaso ba maza (15%) kan mata (4%) a cikin watanni 12 kafin a yi wannan kididdigar.
“Cikin wadanda suke saduwa da wadanda ba matansu ba a watanni 12 da suka gabata, kaso 24% na mata da kaso 45% na maza an samu bayani kan yadda suke amfani da kwararon roba a tarayyarsu.”
A batun shekaru kuwa, masu shekaru 20 zuwa 24 ne suka fi yawa (5.8%) da suke da fiye da abokan tarayya biyu, daga nan sai masu shekaru 15 zuwa 29 sannan 30 zuwa 39 suka zama daidai.
Mata masu shekaru 40 da doriya ne basu kai yawan ba. Binciken ya bayyana cewa mazan da suka fi kudi da ilimi ne suka fi yawa fiye da wadanda ba su da su.
Maza masu shekaru tsakanin 20 zuwa 29 ne suka fi yawa (21.5%) masu abokan tarayya fiye da biyu, sai mazan da ke shekaru 30 da doriya (17%) sannan abokan tarayyarsu yawanci tsakanin shekaru 15 zuwa 19 ne (5.3%).
Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi
Wani ma’aikacin yanar gizo, Chizitere Ahubelem ya janyo cece-kuce yayin da ya bayyana yadda wata mata ta ba shi sharudda kafin ta yarda ta taimaka masa, Legit.ng ta ruwaito.
Kamar yadda ya bayyana, tare da wallafa hirar da suka yi ta WhatsApp, sai da ta nemi kwanciya da shi kafin ta tallafa masa da kudi.
Ya sanar da Legit.ng cewa ya shiga matsanancin rashin kudi ne hakan ya na ya nemi tallafi daga wurinta.
A nan ne yace yana fatan kada Ubangiji ya sanya shi a yanayin da mai taimakonsu zai nemi lalata da shi kafin ya duba masa.