Liverpool ta tashi da ci 3-3 a wasan da ta buga na shida na gasar Premier bana da Brentford a filin wasa na Brentford Community.
Yoane Wissa ne ya jefa kwallo ta uku a ranar Liverpool a minti na 82 da fara wasan abin da ya bai wa kungiyarsa damar kama canjaras da Liverpool.
Tun a minti na 27 da fara wasan Brentford ta samu nasarar zura kwallo guda ta hannun dan wasanta E. Pinnock, wanda daga baya Liverpool ta zare ta hannu Jota aminti na 31.
Salah ya kara kwallo ta biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, a minti na 54, kwallonsa ta 100 kenan a gasar ta Premier.
Liverpool ta ci gaba da matsa lamba wanda ya sa aka yi zaton za ta samu nasara a wasan.
Bayan minti bakwai da wannan kwallo ta Sallah, V. Janelt ya kara farke wa Brentford inda wasa ya koma 2-2.
Jones ya kara ta uku a ragar Brentford cikin wani zazzafan salo daga wajen yadi na 18, koda yake hakan bai kashewa masu masaukin bakin ba jiki.
Liverppol dai ita take jan ragamar gasar da maki 14 a saman abokan hamayyarta Chelsea da Manchester City da United.
Sai dai Brighton & Hove Albion na da damar hawa ta daya a ranar Litinin idan ta yi nasara a wasan da za ta buga da Crystal Palace a filin wasa na Selhurst Park.
A ranar Talata Liverpool za ta buga wasanta na Champion da FC Porto a Portugal, kuma idan ta yi nasara za ta ci gaba da zama a mataki na farko a rukunin B.
A wasan farko ta doke AC Milan ne da ci 3-2 a filin wasa na Anfield, abin da ya mayar da Milan din wadda za ta kara da Atletico madrid ta karshe.