Manchester United ta sha kaye da ci daya mai ban haushi har gida a filin wasa na Trafford a hannun Aston Villa.
Bugun daga kai sai mai tsaron raga da Bruno Fernandes ya zubar a minti na 93 da fara wasan ne ya bai wa Aston Villa wannan dama.
Wannan ce nasara ta farko da Villa ta yi a Old Trafford cikin shekara 12 a wani wasa da aka yi kare jini biri jini tsakanin kungiyoyin biyu.
Kortney Hausene ya jefa kwallon daya tilo da aka ci a wasan a minti na 88, kafin daga baya ya taba kwallon da hannunsa a cikin yadi na 18 wanda ya bai wa United damar samun bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Bruno Fernandes wanda ya saba buga wa United finariti shi ne ya buga ma a wannan karo, sai dai kuma ya tashe ta sama ya gaza ci.
Dan wasan wanda ya ci kusan kashi 93 cikin 100 na finaritin da ya buga a United, ya gaza farke wa kungiyar abin da ya kawo karshen rashin cinye kungiyar da ba a yi ba a wannan kakar.
Bayan kashin da United ta sha a kofin Carabao a hannun West Ham, kungiyar ta yi rashin nasara sau biyu a jere ba tare da jefa kwallo ko guda ba.
Sai da Villa ta samu manyan damarmaki har guda biyu kafin samun nasarar da ta yi a karshen wasan.
Ya zuwa yanzu dai United na da maki 13 a teburin gasar kamar yadda takwarorinta na Manchester City da Liverpool da Chelsea da ta sha kashi a hannu City suke da shi.
A ranar Laraba Manchester United za ta buga wasanta na gasar Champions da kungiyar Sifaniya Villarreal a wasa na biyu na gasar.
A wasan farko na gasar ta yi rashin nasara a hannun Young Boys da ci biyu da daya abin da ya mayar da ita ta karshen teburi a rukunin da take ciki na F.