Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne a ranar Larabar, sun tare hanyar Kachia a kauyen Tashan-Iche, na karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna tare da yin garkuwa da wasu matafiya. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Daya daga cikin matafiyan da suka tsere da kyar, Mista Shuaibu Eneojo ya shaidawa manema labarai a Kaduna a ranar Larabar cewa, ‘yan bindigar sun far wa masu ababen hawan ne da misalin karfe 7:00 na safe inda suka yi awon gaba da wasu mutane da ke kan hanyar a lokacin.
KATANRA WANNAN LABARIN: An Tasa Keyar Tsohon Shugaban Guinea Zuwa Gidan Yari
Ya yi zargin cewa galibin ma’aikata da ke zuwa Kajuru, sun koma gida, biyo bayan toshewar hanyar.
Sai dai har kawo hada wannan rahoton, Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kaduna, DSP Mohammed Jalige, bai tabbatar da faruwar harin ba.
A WANI LABARIN KUMA: Gwamnoni Dake Goyon Bayan Wike, Sun Kauracewa Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Jam’iyar PDP
Biyo bayan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, gwamnonin a dake goyon bayan gwamnan Rivers Nyesom Wike a ranar Laraba sun kauracewa taron kaddamar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyar a hukumance.
Daily Post ta ruwaito cewa, Gwamnonin sun hada da Samuel Ortom na jihar Benue; Seyi Makinde na jihar Oyo; Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu; Okezie Ikpeazu na jihar Abia da shi kanshi gwamna Wike