Rahotanni na nuna cewa, Rundunar hadin gwuiwa a jihar Bauchi ta kama wani likitan jabu bayan wani aikin tiyata da ya yi.
Daily Post ta ruwaito cewa, Wanda ake zargin mai suna, Andrew Godwin, wanda ya fito daga jihar Nasarawa, an kama shi ne a ranar Lahadin da ta gabata saboda wani aiki da yayi wnada bai yi nasara ba kuma ya kai ga mutuwar Joshua Haruna.
KARANTA WANNNA LABARIN: Ana Fargabar Yan bindiga Sun Sace Fasinjoji A Babban Haryar Kaduna
Haruna yana da shekaru 45 kuma mazaunin Gambar Lere ne a karamar hukumar Bogoro na jihar Bauchi.
Majiyar Dimokuradiyya ta ruwairo cewa wanda ake zargin yana zaune ne a Gambar Sabon Layi dake yankin Tafawa Balewa inda yake gudanar da harkokinsa.
Ana zargin mutumin da kasancewa ma’aikacin kantin sayar da magunguna kuma bai sami wata takardar shaidar kwarewa ba a fannin aikin likita ko amincewa ba daga hukumomi.
An yaki wanda aka lamarin ya rutsa da shi a ciki, kuma an bar raunin a bude har washegari, kamar yadda wata majiya daga cikin al’umma ta bayyana.
Al’ummar yankin sun shaidawa DAILY POST cewa Andrew Godwin ya yi wa mutane da dama tiyata da ba su yi nasara ba wadanda daga baya suka mutu.
Wani Jami’in JTF da ya bukaci a sakaye sunan sa ya ce sun kama ma’aikacin kiwon lafiyar na jabu tare da mika shi ga ‘yan sanda da ke sashin Bogoro domin gudanar da bincike.
Marigayin dai ya kasance har zuwa rasuwarsa, tsohon shugaban jam’iyyar APC na gundumar Boi C a karamar hukumar Bogoro kuma kodinetan yakin neman zaben Sanata Lawal Yahaya Gumau ne.
Tuni aka binne shi kamar yadda addinin Kirista ya tanada.
A WANI LABARIN KUMA: Gwamnoni Dake Goyon Bayan Wike, Sun Kauracewa Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Jam’iyar PDP
Biyo bayan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, gwamnonin a dake goyon bayan gwamnan Rivers Nyesom Wike a ranar Laraba sun kauracewa taron kaddamar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyar a hukumance.
Daily Post ta ruwaito cewa, Gwamnonin sun hada da Samuel Ortom na jihar Benue; Seyi Makinde na jihar Oyo; Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu; Okezie Ikpeazu na jihar Abia da shi kanshi gwamna Wike