Daga Mustapha Musa Sarkinfawa
Mai rikon konturola na hukumar Kwastom a shi ya ta daya wato (zone A) Hussein Ejibunu, yayi gargadin cewa ‘yan bindiga da masu fasa kwabri ta haramtacciyar hanya na kai wa jami’an su farmaki musamman a yankin Kudu maso Yammacin kasar.
Da yake yi wa manema Labarai jawabi a shelkwatan yanki na hukumar a garin Legas, Ejibunu ya kara da cewa, yankunan da akafi samin aikata laifuffka sun hadar da Ado-Odo da Idogo, Sokoto-ljoun da Ohunbe da Ilaro da Atan da Abeokuta/Sagamu Interchange da ljebu-Ode a jihar Ogun, Gbaji sauran sun hadar da Agbara a jihar Ogun Iseyin da Igboora da kuma Igbeti a jihar Oyo,amma babban inda ya zaman tungan masu aikata laifuffka shine yankin gabar kogin Ologojo dake kan iyaka da jamhoriyar Benin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abin da ya sa nake Tsinuwa a Fim, inji Musa Maisana’a
Ejibunu ya kara da cewa ganin hakan tuni hukumar ta samar da runduna ta musamman dazata fatattakin bata garin.
A wani labarin Kuma na daban .
Ma’aikatar lafiya ta jihar Nasarawa tace sama da mata guda 9,000 ne a jihar a halin yanzu suke yin allurar rigakafin tsarin iyali a jihar.
Shugaban gudanarwa na shirin tsarin iyali a ma’aikatar lafiya ta jihar Nasarawa, Misis Salome Aya itace wacce ta bayyana hakan a birnin Lafiya inda tayi bayanin cewa ana yin hanyar allurar kai a cikin yankunan karkara da birane na jihar.
A cewar ta, taron bitar tsarin iyalin mata 9,700 a halin yanzu suna amfani da samfurin tsara iyali.Misis Aya tace samfurin ya wanzu tun kafin yanzu amma ana kula da shi ne kawai a cikin tsarin tsara iyali ta hanyar lafiya.
“Wannan samfurin yana da tasiri sosai kuma yana da sauƙin gudanarwa.Duk abin da matan ke buƙata su yi shi zuwa kowane ɗayan cibiyoyinmu a cikin Kananan Hukumomin 13 na jihar kuma za a ba su samfurin kyauta ”.
Sannan tace tare da kayan allurar kai, matan jihar ba za su buƙaci kasancewa a wuraren ba koyaushe musamman waɗanda ke nesa da wuraren saboda rashin tsaro.baya da haka tayi kira ga mata da maza a jihar Nasarawa dasu karfafa gwiwar ma’auratan su dasu yi aikin bada tazarar haihuwa don baiwa matan su damar samun lafiya mai kyau tare da taimakawa wajen rage mace -macen mata masu juna biyu a fadin jihar.
Kazalika Aya ta kuma yabawa gwamnatin jihar da dukkan masu ba da gudummawa don tallafawa hangen nesan rage mace -macen mata masu juna biyu a tsakanin iyaye mata da matasa a Nasarawa.