Wani Mamallakin wani Katafaren Otal a Najeriya ya bayyana cewa yanzu tura ta fara kai su bango bisa irin yadda ake musu awon gaba da majanyin bayan gida wato Tawul.
Mutimin ya ce cikin watanni uku kachal an sace muau tawul kimanin dari shida, wanda kuma hakan ya fara wuce muau wuya.
Cikin sakon da ya wallafa a shafin sa na Instagram dake dauke da suna @officialKoya, ya ce wata kila mutane na so su bijiro da dabi’ar chaje jaka ce ga duk wanda ya kwana hotel ɗin, don gudun kitso da Ƙwarƙwata.
Ya ce “Ta ya za mu Magance matsalar sace-sace a otal musamman na Tawul?
“A cikin watanni uku kachal mun maye gurbin tawul kimanin dari shida, ko dai za mu fara chaje Jakar mutane ne, ko kuma mu daina kawi tawul?
To sai dai wannan lamari ya janyo sharhi da dama daga mabiyan sa, wadanda akasari suka maida batun ya zamo raha.
Wani mai suna @lollypeezle ya ce naka mai sauki ne, domin wasu har maratayin kaya ko kuma kwaba suke dauka.
Shi kuwa wani mai suna @espeezeal cewa ya yi da ma kamata ya yi tawul ya zama ribar kafa musamman a otal din alfarma irin naku da kudinsu ya wuce tunanin mutum.
Kawo yanzu dai babu wani martani daga bangarne Mamallaka ota-otal a kasar nan kan ko shawarar tashi ta chaje Jakar mutane za ta karbu