By Ishaq Dabai
Rundunar sojojin samar da zaman lafiya ta OPSH ta jihar Plateau a ranar Juma’a da daddare ana zargin sun yiwa wani direban taxi dukan kawo wuka mai suna Sadik Abdullahi Karafa inda yayi sana diyyar mutuwar sa.
Rahotonni sun bayyana cewa dukan da jami’an sojojin suka yi masa a wurin shingen bincikesu na kasuwar Paringada a kan hanyar sa ta dawowa daga Mangu kafin lokacin dokar hana zirga zirga ta fara aiki, dokar hana zirga zirga dai tana farawa ne daga karfe 10 na dare zuwa 6 nasafe inda shi Sadik ya dawo gida wajejen karfe 9:20 daren ranar.
Abdullahi Karafa wanda yayane ga Sadik, ya bayyana cewa taya sojoji suka kashe masa dan uwansa.sannan yace yana gida sai wani dan uwansa ya kirashi cewa an kama dan uwansa sojoji suna dukansa a kusa da titin Paringada, inda shi kuma ya sanarwa da karamin kaninsu inda yaje ya tarar sojoji suna ta dukansa.
“A yayin da yake fada musu cewa Sadik dan uwansa ne ko kulashi basuyi ba inda suka dauke shi suka sashi abayan Hilux dinsu, sai ya dawo gida ya sanar wa da ‘yan uwansa cewa su bari sai da safe suje sujiyo dalili tunda a lokacin dokar hana zirga zirga yayi, inda washe garin ranar Asabar suka je Faringada da zuwansu suka tarar ya mutu.
“Sannan mukaje muka kai gawarsa zuwa ofishin ‘yan Sanda na Katako dan shigar da korafin faruwar hadarin, har zuwa yanzu babu wani martanin dalilin mutuwar sa, sai dai Babban jami’in ‘yan Sanda na shiyya ta 3 ya ziyarci iyalan mamacin inda yayi musu alkawarin za’ayi musu adalci kuma bazasu bar ‘abin yatafi haka ba,”a cewar sa.
Koda aka tuntubi mai magana da yawun Rundunar ta OPSH Ishaku Takwai yace zai bincika tare da bayar da ba’asi tunda shi bayanan a lokacin da abin ya faru.
Comments 1