By Abbas Yakubu Yaura
Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Pius Anyim, ya yabawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari bisa rattaba hannu kan dokar gyara zabe a ranar Juma’a.
A wata sanarwa da ta fito daga ofishin yada labaran sa mai dauke da sa hannun Sam Nwaobasi a ranar Juma’a, Anyim ya yabawa Buhari kan yadda ya yi kamar shugaban kasa mai kishin kasa ta hanyar sanya hannu a dokar.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya lura cewa “yana bukatar mutumin da ya jajirce wajen ganin Najeriya ya rattaba hannu kan kudirin dokar duk da rashin amincewa da wasu tanade-tanade na kudirin.”
Anyim ya kuma bayyana cewa “idan ba a kafa dokar zabe ba, gudanar da zaben 2023 zai kasance cikin hatsari.
“Tuni kasar nan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa sun yi kunnen uwar shegu game da jinkirin da aka samu na sanya hannu kan dokar kafin ranar Juma’a.
Anyim ya kara da cewa, “Tare da dokar zabe, an dauki wani muhimmin mataki na gudanar da sahihin zabe a shekara mai zuwa, domin hukumar zabe ta INEC, da jam’iyyun siyasa, da masu takara da sauran masu ruwa da tsaki a halin yanzu suna da takardar doka da za ta jagorance su.”