Arsenal na duba yuwuwar daukar kociyan Leicester City Brendan Rodgers ko Christophe Galtier na Nice idan ta yanke shawarar sallamar Mikel Arteta. (Transfer Window Podcast, ta Teamtalk)
Manchester City ta kara da sunan dan wasan Borussia Dortmund na tsakiya Jude Bellingham a cikin jerin ‘yan wasan da take son saye kuma za ta kalubalanci Liverpool a kan matashin dan Ingilar mai shekara 18. (Star on Sunday)
Dan gaban Norway da Borussia Dortmund Erling Braut Haaland, mai shekara 21, ba shi da niyyar gaggauta yanke hukunci a kan kungiyar da zai tafi, idan lokacin damar sayar da shi ta biyan kudin na-gani-ina-so fam miliyan 70 ya yi a 2022. (90 Min)
KARANTA WANNAN LBARIN: Fim din Labari na me ya daga Daraja na, inji Abdullah Amdaz
Kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti, ya ce babu wata damuwa da kungiyar ta yi bayan da ta kasa samun daukar dan gaban Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, daga Paris St-Germain a lokacin kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta bazara da aka rufe. (Goal)
Kociyan Chelsea Thomas Tuchel ya ce shawara ce mai saukin gaske da suka yi kan kin barin dan wasansu na gaba na gefe dan Ingila Callum Hudson-Odoi, mai shekara 20, ya tafi a rana ta karshe ta kasuwar sayar da ‘yan wasa ta bazara. (Football London)
Barcelona ta ki yarda ta dauki dan wasan tsakiya dan Faransa Tanguy Ndombele, mai shekara 24, da dan bayan Ivory Coast Serge Aurier, mai shekara 28, a matsayin yarjejeniyar da kungiyar ta sayar wa Tottenham dan bayanta, dan Brazil Emerson Royal. (Fabrizio Romano ta Sunday Express)