An biya ma’aikatan kamfanin matatar mai NNPC mallakar gwamnatin Tarayyar Nigeria, jimillar Naira biliyan 69.07 a shekarar da ta gabata, duk da cewa, kamaiyar Kamfaninin ba su samar da kudin shiga ba, kamar yadda ba su sarrafa gangar danyen mai ko guda ba.
Matatun sun yi asarar naira biliyan 108.29 a shekarar 2020, idan aka kwatanta da Naira Billiyan 162.22 a shekarar da ta gabata, kamar yadda bayanan da aka tattara daga bayanan kudaden kamfanin NNPC ya fitar ranar Laraba.
Matatun mai dake Fatakwal, Kaduna da Warri, suna da ƙarfin tace ganga mai 445,000 a kowace rana, amma ba sa iya wa, sakamakon lalace wa da su kayi a shekaru da dama.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fim din Labarina ne ya daga Darajana, inji Abdullah Amdaz
Kamfanin matatar mai na Kaduna ya ba da rahoton asarar Naira Billiyan 55.77 a bara; yayin da Kamfanin tace Mai na Fatakwal ya yi asarar Naira billiyan 28.67; Kamfanin dake Warri kuwa, Shima ya yi asarar Naira Billiyan 23.85.
Albashin wata-wata, da na mako mako, da sauran wasu tsarabe-tsarabe da aka biya ma’aikatan matatar Man Kaduna, ya Kai Naira Billiyan 26.02 a shekarar 2020, daga cikin Naira Billiyan 34.52 na bara.