A yunƙurin gyara da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal dake ci gaba da yi wajen yin garambawul domin ganin ta koma gidan jiya wajen lashe manyan gasa kamar gasar ajin Firimiyar ƙasar Ingila data kwashe shekaru masu yawa bata lashe ba.
Haka zalika ƙungiyar ta Arsenal ta shiga yanayi ba tare da tazo gasar zakarun nahiyar turai ba inda sai gasar ajin ƙwararru take zuwa wanda hakan ba ƙaramin koma baya bane awajen ƙungiyar ta Arsenal.
Hakan yasa a daren jiya ta sayi sabon mai tsaron gida domin sake inganta yadda za’arage jefamusu ƙwallo a zare inda ake zaton mai tsaron gidan zai basu gudun mawa sosai da sosai misamman a kakar wasa ta bana da kusan kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa tayi gyara.
Arsenal dai mai tsaron gidan data saya shine Alex Runarsson kuma tuni ya dira a ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Arsenal tun a daren jiya kenan.
Arsenal dai ta lashe wasanninta guda biyu na gasar ajin Firimiya data buga inda awasan farko ta casa Fulham daci 3 da nema sannan kuma sukasha da kyar a hannun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta West Ham United.