Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa ASUU ta ce kuskure ne mai girma a ce gwamnatin tarayya ta baɗa wani muƙami a kungiyar ga wanda ba shi da digiri ko guda ɗaya.
Shugaban kungiyar matakin kasa Farfesa Emmanuel Osodeke shine ya yi wannan batu yayin da yake tattaunawa da jaridar Tribune.
Kazalika ya ce Matsayin bai sauya ba ga dukkannin gwamnatocin jihohi, la’akari da matsayinsu a harkar ilmi.
A cewarsa duk wani wanda za a naɗa shi a muƙamin kujerar jami’ar tarayya tilas ne ya kasance yana da digiri na farko, kamar yadda yarjejeniyar ƙungiyar ASUU ta cimma da gwamnatin tarayyar.
Ya yi bayanin cewa ba zai zamo haufi ba ga duk wani wanda ya san bashi da wata kwarewar wajen gudanar da harkokin mulki da ya janye kafafunsa daga hidimar, don haka dole ne a girmama shugabanci.
Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce Ƙungiyar ASUU ba za ta lamunci wannan cin fuska da ake mata ba, musamman yadda ake ɗaukar wasu yan siyasa ana dora su a mukami mai tsantsaini irin wannan.