Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi shiru kan rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Saraki wanda ya rufe baki tun bayan rasa tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar wanda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a ranar 28 ga watan Mayu ya kada shi, a ranar Asabar, ya bayyana cewa ya tafi hutu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Najeriya Ba Tada Matsalar Talauci Da Tsaro, Sai…. Inji Obasanjo
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter @bukolasaraki ya ce, “Na dawo daga hutuna na shekara na wuce kai tsaye zuwa jihar Akwa Ibom domin halartar bikin cika shekaru 35 da kafa jihar.”
A wani sakon tweeter ya bayar da wata alama game da shawararsa na kin yin magana kan abubuwan da ke faruwa a PDP.
Ya ce, “A yayin da na zagaya kasar cikin ‘yan kwanakin nan, na ji cewa mutane da yawa sun damu da yadda na yi shiru kan abubuwan da ke faruwa a jam’iyyarmu ta PDP.”
“Amsa ta ita ce cewa akwai lokutan magana da ji kuma akwai lokutan da yin aiki shiru a bayan fage ya fi fa’ida. Wannan shi ne irin wannan lokaci.”
“PDP da Atiku Abubakar sun kasance su suka fi cancanta su zama zabin ‘yan Najeriya a zaben 2023.”
A wani labarin kuma, Zabukan 2023 Zasu Bambanta Da Na 2019 – INEC Ta Fadawa Yan Najeriya
Yayin da zabukan shekarar 2023 ke kara karatowa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta ce za a samu ci gaba wajen gudanar da zaben.
Kwamishiniyar INEC ta kasa mai kula da sa ido da tsare-tsare (PMSC), Farfesa Rhoda Gumus ce ta bayyana hakan, yayin wani taron bita na yini biyu kan Cibiyar Sa ido da Tallafawa Zabe (EMSC) ga shugabannin Sassan Hukumar (HODs) a jiya a jihar Gombe.