Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Asabar din nan ya gana da ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar daga sassan kasar nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Tsohon mataimakin shugaban kasar tare da abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta, sun gana da ‘yan takarar a gidansa da ke Asokoro, da ke Abuja.
Karanta kuma: Atiku, Da Gwamnonin PDP, Zasu Ziyarci Wike A Wani Yunkurin sulhuntawa Da Shi
Wadanda suka halarci taron sun hada da ‘yan takarar gwamna daga jihohin Kaduna, Plateau, Katsina, Lagos, Niger, Kano, Sokoto, Delta, Yobe, Jigawa, Nasarawa, Kwara, Benue, Borno, Ebonyi da Zamfara.
Gidan talabijin na Channels ta rawaito cewa, An gudanar da taron ne a sirri gida.
A wani labarin kuma: EFCC Ta Saki Wani Kakakin Majalisa Bayan Awanni 48 Da Kama Shi
Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta saki kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo bayan shafe sa’o’i 48 a hannun ta.
Oluomo dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Ifo ta 1 a majalisar dokokin jihar Ogun ya koma gidansa dake Ifo a safiyar ranar Asabar din nan.