Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da harin jirgin kasa na Edo, yana mai cewa “tunawa ne a kan bukatar gaggawar sake fasalin tsarin tsaron mu domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.”
Ku tuna cewa sama da fasinjoji 30 da ma’aikatan hukumar kula da layin dogo ta Najeriya (NRC) ne ake kyautata zaton an sace sakamakon farmakin da masu garkuwa suka kai a daren ranar Asabar a tashar jirgin kasa ta Igueben da ke jihar Edo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ziyarar Buhari: Gwamnatin Yobe Ta Ayyana Ranakun Hutun A Jihar
Da yake mayar da martani, Atiku, a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran sa ya sanyawa hannu a ranar Lahadi, ya lura cewa wannan mummunan abu ne “shine na baya-bayan nan a cikin jerin tashe-tashen hankula na tsaro da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasarmu.”
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya yi addu’ar Allah ya dawo da su lafiya, yana mai cewa “yin amfani da matsin lamba na diflomasiyya da ake bukata don dakile kwararar makamai masu linzami a yankin yammacin Afirka da kuma iyakokinmu.
A wani labarin kuma, Wasu Kawayen Juna Sun Shiga Rudani Bayan Sun Samu Juna 2 Lokaci 1
Wata ‘yar Najeriya mai suna Atinuke Dami-Yakubu ta bayyana cewa ita da babbar kawarta sun samu juna biyu a lokaci guda.
Atinuke, wadanda suka raba hotunan haihuwarsu a shafin Facebook a ranar Lahadi, 8 ga watan Janairu, 2023, sun ce ba su shirya daukar ciki ba.