Gwamnatin jihar Yobe ta ayyana ranakun Litinin 9 da Talata 10 ga watan Junairu, 2023 a matsayin ranar hutu yayin da shugaba Buhari ya kai ziyara jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan 8 ga watan Janairu, 2023, kuma mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikata na jiha, Alhaji Garba Bilal.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Kawayen Juna Sun Shiga Rudani Bayan Sun Samu Juna 2 Lokaci 1
Ya ce, “Wannan ne don baiwa dukkan ma’aikatan gwamnati da sauran jama’a damar tarbar shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, wanda zai kai ziyarar kwana guda a jihar yayin da yake kaddamar da ayyukan raya kasa a jihar. ”
A cewar sanarwar, dukkan ma’aikatan gwamnati za su koma bakin aiki ranar Laraba 11 ga watan Janairu, 2023.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa a jihar Yobe, shugaba Buhari zai kaddamar da sabon filin jirgin saman dakon kaya da aka kammala na Yobe, da dai sauransu.
A wani labarin kuma, FG Ta Fitar Da Jerin Sunayen ‘Yan Takara 20 Don Maye Gurbin Tsohon Akanta Janar
Gwamnatin tarayya ta fitar da jerin sunayen mutane 20 da za su fafata a matsayin sabon babban akanta janar na tarayya, AGF, a cewar wata kafar intanet, TheCable.
‘Yan takarar guda 20, a cewar wata takardar da gwamnati ta fitar, an zabo su ne daga ma’aikatu, da hukumomi, MDAs.