• Ana samun raguwar masu kamuwa da cutar korona a Nijeriya
• Ba asami ko mutun daya ba, daya kamu da cutar korona a Nijeriya.
• Babu wanda ya mutu a awa 24 da ya gabata.
Haryanzu a na cigaba da samun karancin masu kamuwa da cutar korona a Nijeriya, biyo bayan sanarwar da cibiyar kula da dakile yaduwar cututtuka ta kasa wato NCDC ta fitar, na cewa, inda ta ce, wadanda su ka kamu da cutar sun kai, 167,206 a fadin kasar nan.
A cikin shafin ta na yanar gizo, cibiyar ta NCDC, ta ce, an samun raguwar masu kamuwa da cutar a Nijeriya.
Cibiyar ta ce, babu wani rahoton bullar cutar a ranar 20 gawatan Yunin shekarar nan, sai dai rahoton ba a hada shi dana jihar Legas ba.
Sanarwar da cibiyar NCDC ta fitar ya kuma nuna cewa, an sallami mutun 7 daga wurin killace masu cutar korona.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ifeanyi zai fa-fa-ta a zaben gwamnan jihar Anambra
Kazalika hakan ya sa, adadin wadanda aka sallama ya Kai 163,577, daga cikin rahoton mutun 167,206 da aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin kasar nan.
A karshe NCDC ta bayyana cewa, ba a sami ko mutun daya da ya mutu sanadiyar cutar ba, a tsakanin awanni 24 da su ka gabata.