A jiya lahadi ne kungiyar yan jaridu ta kasa NUJ reshen jihar Oyo, ta bukaci gwamna Seyi Makinde, da hukumomin tsaro, da su binciko wadanda ke da hannu a kisan wani dan jarida mai suna Titus Badejo, da a ka harbe shi a daran ranar asabar a biirnin Badun.
Kungiyar ta fitar da sanarwar ce, ta hadin gwuiwar Shugaban kungiyar Alhaji Ademola Babalola, da sakataran ta Kwamared Sola Oladapo, inda ya bayyana cewa, a na samun karancin tsaro a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba a sami ko mutun daya ba da ya kamu da korona a Nijeriya
A cewar kungiyar ta NUJ, kisan na da ke samu jihar abun ta kaici ne, inda kuma ta yi kira ga al’umar jihar da su kula matuka akan lamarin.
Kazalika, “muna amfani da wannan dama wurin sake yin kira ga gwamnan jihar, kwamishinan yan sandan, dama sauran masu ruwa da tsaki, dasu binciko wadanda ke da hannu a kisan dan jaridan, da wasu da aka kashe, a cikin wannan lokacin” inji kungiyar.