Gwamnan Jahar Katsina Aminu Bello Masari ya ƙaryata jita-jitar dake yawo cewa ya yi taro da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Landan kan rikicin Shuwagabancin Jam’iyyar APC dake faruwa a halin yanzu.
Dayake jawabi ga Manema Labaru a Gidan Gwamnati dake Katsina a ranar Litinin da yamma, Muƙaddashin Darakta-Janar na Gwamna Masari akan Kafafen Yaɗa Labaru Al-amin Isa, ya bayyana jita-jitar a matsayin labarin ƙanzon kurege, kuma ƙirƙirarre ga waɗanda suka shirya shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanata Uba Sani Ya Bayyana Aniyar Tsayawa Takarar Gwamnan Jihar Kaduna
Akwai Jita-jita a Katsina dake Yawo cewa, Gwamnan yayi tafiya zuwa Landan domin neman Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya Kawo ƙarshen Rikicin Shuwagabanci daya dabaibaye Jam’iyyar APC.
Amma Isa, a lokacin zantawar sa yace “dalilan yi maku jawabi a yau (Litinin) shine domin mu ƙaryata jita-jitar dake yawo cewa Gwamna Masari yaje Landan domin ya nemi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen rikicin APC.
“Muna son mu sanar cewa Gwamna bai je ko’ina ba a ƴan kwanakin nan. Kuma Dukkanin jita-jitar dake yawo ƙirƙira ce ga waɗanda ke yaɗa ta.”
A cewar Muƙaddashin Darakta-Janar na Masari akan Kafafen Yaɗa Labaru “mai Girma Gwamna baije ko’ina ba, kuma baije Landan ba, kamar yadda mutane suke yaɗawa.