Sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattijan Nageriya Sanata Uba Sani ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kaduna.
Sanatan ya bayyana aniyarsa ne a Sakatariyar Jam’iyyar APC na jihar, gabanin babban zabe na Kasa mai zuwa na shekarar 2023.
A yanzu dai, Sanatan da ya kwashe shekaru uku yana wakiltar Kaduna ta Tsakiya a majalissar Dattawan, kana ya na shan yabo daga Al’umma daban-daban na jihar Kaduna.
A jawabin nasa, ya yi alkawarin dorawa tare da “gina kyakkyawan tsarin mulkin irin na gwamna mara gajiyawa, mai samar da kirkire-kirkire da wadata, wanda ba ya misaltuwa, watau Malam Nasir El-Rufai. ” Inji shi.
“Mallam El-Rufai ya canza fasalin jihar Kaduna. Ya sake fasalin mulki ta hanyar samar da ababen more rayuwa da ba a taba ganin irinsa ba da magance kalubalen dake kawo na kasu a ci gaban jihar. Ya daga darajar shugabancin jihar “inji Sanatan.
Sanatan ya kara da cewa, “El rufa’i babban mai imani ne akan falsafar mulki na karanta shi tsawon shekaru da yawa.”
“Zan tsaya a bisa kyakykyawan matsayi na dorewa ga shimfida iyakoki na kyakkyawan shugabanci a wannan jiha tamu mai albarka. Na kasance mai nasara. Na nuna hakan a Majalisar Dokoki ta Kasa. Ina mai kishin jin dadi da ci gaban al’ummar jihar Kaduna. Ina Kuma sanarwa a yau cewa, na kulla yarjejeniya da daukacin al’ummar jiharmu mai ma’ana da albarka da girmamawa.”
A Karshe Sanatan ya mika godiyarsa ga jama’a magoya bayansa, inda ya ce, “Ina nuna godiya ga shuwagabannin kananan hukumomi na babbar jam’iyyar mu, ‘yan majalisar jiha da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da suka yi tafiya tare da ni zuwa sakatariyar jam’iyyar ta jiha domin gabatar da shela ta, a cikin farin ciki da magoya bayan jam’iyyar da ‘yan jihar Kaduna suka yi. A bisa gagarumin aikin da shuwagabannin jam’iyyar APC na jihar Kaduna da shugabannin kananan hukumomin na jam’iyar suka yi, na ba su gudummuwar motoci guda 59 don taimaka musu wajen saukaka ayyukansu da kuma zaburar da su don tunkarar yakin babban zabe na 2023.
“Ina kira ga al’ummar jihar Kaduna da daukacin magoya bayanmu da masu fatan alheri da su zo tare da ni a wannan tafiya ta hadin gwiwa. Iko naka ne. Zan zama bawanka. Zan baku kyakkyawan sakamako, za mu yi hadin gwiwa a kan manyan ayyuka na Gwamna El-Rufa’i. A yayin da muke kokarin bude sabbin kofofi mu na addu’a Allah madaukakin Sarki ne zai zama jagora da garkuwarmu. A gare shi ne ƙarfinmu yake.” A cewar Sanata Uba Sani.