Wani dan Najeriya ya bayyana a soshiyal midiya inda ya nuna wani hamshakin gidansa mai fili mai matukar yalwa, Legit.ng ta ruwaito.
Kamar yadda ya bayyana hakan cike da alfahari, ya sanar da sirrin daukakarsa inda ya ce yana kyautata zaton wannan ne ya sa ya samu dukiya mai yawa.
KU KARANTA: Hotunan matashin ya yi ankon suttura da karensa ya sa shi a gaban mota ya ɗauki hankula
Nan da nan mutane suka hau cece-kuce akai, wasu sun aminta da cewa tabbas wannan lakani ne, yayin da wasu suke wasuwasi.
Kamar yadda ya bayyana a wani sabon bidiyon TikTok, ya fara da nuna harabar gidansa ne tun daga asalin kofar shiga.
Ya ce akwai abubuwa da dama da suka tallafa masa har ya kai wannan matakin na rayuwa. Ya rubuta cewa:
“Saboda ba na shayeshaye. Ba na zuwa gidan rawa. Ba na shan giya. Ba na neman mata.”
A wani bidiyonsa na baya ya bayyana yadda aka yi garkuwa da mahaifinsa a shekarar 2010 saboda tsabar hassadar da ake yi masa. Biloniyan ya ce mahaifinsa ya yi matukar fuskantar kalubale mai yawa.
Uwa Ta Gari: Wata Mata Ta Ƙi Karɓar Kyautar Motar Da Ɗan Ta Yayi Mata, Ta Bayar Da Dalili
Matar dai ta ƙi amsar kyautar motar da ɗanta yayi mata domin taya ta murnar zagayowar ranar haihuwarta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
An nuna lokacin da matar ta ƙi amsar kyautar ne a cikin wani bidiyo da Maria Ude Nwachi ta sanya a shafin ta na Facebook.
Matar ta zargi ɗanta da yin damfarar yanar gizo inda ta koka kan cewa yayi niyyar yayi amfani da ita domin yin tsafi duba da irin yanayin kyautar da yayi mata.