Wata mata ƴar Najeriya ta ba ɗanta, abokan sa da mutane da dama a yanar gizo bayan taƙi amsar kyautar da yayi mata.
Matar dai ta ƙi amsar kyautar motar da ɗanta yayi mata domin taya ta murnar zagayowar ranar haihuwarta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: An kuma: Ƴan bindiga sun sake sace ɗalibai a Arewacin Najeriya
An nuna lokacin da matar ta ƙi amsar kyautar ne a cikin wani bidiyo da Maria Ude Nwachi ta sanya a shafin ta na Facebook.
Matar ta zargi ɗanta da yin damfarar yanar gizo inda ta koka kan cewa yayi niyyar yayi amfani da ita domin yin tsafi duba da irin yanayin kyautar da yayi mata.
Duk da ƙoƙarin da matashin da abokan sa suka yi domin ganin ta karɓi kyautar, ta ƙi karɓa inda ta umurce shi da ya ɗauke motar ya tafi da abarsa, yayin da ta faffasa balo-balon da aka yiwa motar kwalliya da su.
A cewar ta har yanzu karatu yake yo a jami’a kuma baya da aikin yi saboda haka bai isa ya samu irin wannan motar ba.
“Ɗalibi ne kawai kai fa. Wane aiki kake yi” Ta gaya masa.
Yayin da mutane da dama suka yabawa matar, wasu sun yi tunanin cewa shiri ne kawai duba da yadda ta riƙa sunan ɗan nata.
Ƙilu Ta Janyo Bau: Kotu Ta Umurci Budurwa Biyan Maƙudan Kuɗaɗe Bayan Ta Cinye Kuɗin Saurayi
A wani labarin na daban kuma, wata kotu ta umurci wata budurwa ta biya maƙudan kuɗaɗe bayan ta lashewa wani saurayi ƴan kuɗaɗen sa.
Wata kotu a birnin Enugu ta umurci wata budurwa da ta biya wani mutum naira ɗari da hamsin (N150k) bayan ta amsar masa naira dubu uku (N3k) da niyyar cewa zata ziyarce shi a gida amma ta ƙi zuwa.
Wani lauya mai amfani da @Egi_nupe_ wanda ya sanya labarin a Twitter, yace budurwar ta kashe wayarta bayan ta karɓi kuɗin wanda hakan yaa fusata mutumin.