Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce sake fasalın kasar kawai ba zai magance dimbin matsalolin da suka dabaibaye ta ba, inda ya bukaci al’ummar kasar da su lalubo wasu hanyoyin na daban da za a yi amfani da su wajen shawo kan su baki daya.
Jonathan ya ce ci gaba da muhawara kan wannan batu ba zai taimaka ba, domin kuwa dole sai ‘yan Najeriya sun sake fasalin tunaninsu da kuma irin gudummawar da za su bayar wajen gina kasa.
Tsohon shugaban ya bayyana hakan ne wajen taron da Jaridar ‘Daily Trust’ ta shirya domin tattauna batutuwan da suka addabi Nijeriya a yau.