Rahotannin sun nuna yadda a bara ma gwamnatin jihar ta mayar da wasu almajirai garuruwansu, inda ta zarge su da yaɗa korona.
Zargin da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum suka yi fatali da shi, suka kuma kalli lamarin a matsayin tozarci da cin fuskar almajirai da suke barin garuruwansu su je koyon karatun Alkur’ani mai girma. “ana son fakewa da batun na korona ne a hana karatun Alkur’ani a makarantun allo a fadin jihar”, inji Abubakar Muhammad daya daga cikin mazauna garin Kaduna.
Har wala masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun kalubalanci gwamnan jihar ta Kaduna, Nasir Elrufai da rashin gaskiya. Inda suka ce tabbas an take ‘yancin almajiran na hakkin da suke da shi na zabar inda za su nemi ilimi da kuma zama; “sannan me yasa aka zabi dare aka je aka tattara daliban a daidai lokacin da suke kwance ba tare da sanar da hukumar makarantar za a yi hakan ba?” inji wani da ya nemi mu sakaya sunansa.
Ya ci gaba da cewa; “me yasa aka zabi makarantar Shaikh Dahiru Bauchi a daidai wannan lokacin? Me yasa ba a fara da wadansu makarantun ba?”, ya tambaya.
Shi ko Muhammad Sani, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a garin Kaduna ya caccaki matakin gwamnatin, inda ya ce; “wannan lamari an yi shi ne kawai domin a ci fuskar Shaikh Dahiru Bauchi. Me yasa ba a fara tattaunawa da shi ba kan batun almajiran? Me yasa a ka bi dare aka kwashe su? Wannan ya nuna akwai wani makirci a kasa da ake shiryawa ‘yan Dariku a arewacin Nijeriya. Domin a bayyane yake suneaka san sun yi fice wajen karantar da littafi mafi girma a addinin Musulunci wato Alkur’ani a makarantun allo. Kawai ana fakewa da guzuma ne domin a harbi karsana”, inji shi.
Haka zalika, Usman Adamu wani mazaunin Jihar Kaduna, kuma mabiyin Darikar Tijjaniyyah a yayin da yake zantawa da wakilinmu kan ra’ayinsa bisa tattara almajiran cikin dare, ya bayyana mana cewa; “ni ban yarda saboda dakile cutar korona ne aka kwashe daliban ba. Dama gwamnatin nan tun farko ba ta son ma’abota darikar Tijjaniyyah, idan ka lura da kyau su wa gwamnatin ta fi jawo wa a jika tana tafiya da su? Duk idan ka duba za ka ga ‘yan Izalah ne da suke kiran ‘yan Darika mushrikai suke kuma gaba da karatun Alkur’ani a makarantun Allo sune suke zagaye da gwamnatin. A hankalce za ka iya gane tasirin shawarwarin ko su wane ne! Ba sai na fada maka ba. Ba komai suke son yi ba illa dakushe tasirin Darika wanda hakan kuma ba za su yi nasara ba. Da yake sun ga ana zuba musu ido ne kan duk abin da gwamnatin ta rika yi kan wasu ba’adin Musulmi a jihar, shiyasa suke so su zunguri ‘yan darika su ji ko akwai wurin yankawa, sai su danne su yanka”. Ya tabbatar.
Shi ko Salisu Muhammad, ya shaida wakilinmu cewa; “wannan kawai yunkuri ne na yaki da karatun Alkur’ani mai girma. Ba abin da gwamnan nan ba zai iya ba domin farantawa wasu sashen mutane. Ku lura da kyau duk Nijeriya wanne gwamnan ne ya dakile Musulmi daga yin sallah a masallatai ciki harda sallar Juma’a a tsawon fiye da wata hudu a kaf Nijeriya da sunan yaki da Korona idan ba shi ba? Makiyin mutanen kirki ne, amma ka san an ce sai ka bata sunan kare sannan zaka iya buge shi, wannan shi ne abin da yake yi. Wannan kawai shi ne ra’ayina”.