Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da zabin sakin Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra wato (IPOB).
Wasu shugabannin kabilar Ibo sun ziyarci shugaban a Aso Rock, inda suka roki a sako shugaban kungiyar na IPOB, wanda a halin yanzu yake fuskantar shari’ar cin amanar kasa.
Sun roki shugaban kasa ya tausayawa Kanu, kuma ya yi alkawarin ganin abin da zai iya yi wajan ganin an sake shi.
Sai dai da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels, Buhari ya ce ba zai tsoma baki a harkokin shari’a ba.
“Akwai wata cibiya da ba zan tsoma baki a cikinta ba, wato bangaren shari’a, lamarin Kanu na bangaren shari’a ne, amma abin mamaki shi ne, lokacin da Kanu ya zauna a Turai, yana cin zarafin wannan gwamnati da kuma ambaton abubuwa da yawa, na dauka yana so ne, ya zo ya kare kansa a kan zarge-zargen da yake wa Gwamnatin.
“Don haka muna ba shi damar kare kansa a tsarinmu, ba wai ya rika cin zarafin mu daga Turai kamar ba dan Najeriya ba. Bari ya zo nan tare da mu sannan ya kushe mu a nan. ’Yan Najeriya sun san ba na tsoma baki a harkokin shari’a, don haka a saurare shi. Amma masu cewa a sake shi, a’a, ba za mu iya sakin shi ba.”