A wani mataki na tsaftace harkar hada-hadar kudade tsakanin yan Najeriya da yan kasuwa, Babban bankin Najeriya CNN ya dakatar da saida kudaden kasashen waje wa yan kasuwa.
Yayin wani taron kwamitin shirin bada lamuni da ya gudana a Abuja Gwamnan Babban Bankin Mista Godwin Emefiele ya ce yan kasuwar sun bijirewa tsare tsare da dokokin da aka gindaya musu.
Kazalika ya ce yan kasuwar sun faɗa wata dabi’a ta cushe gami da rufta da ciki da wasu kudade.
Mista Emefiele ya kara da cewa yan kasuwa sun kuma ɓuge da yin kashin dankali wajen hada hadar tasu, don haka dole ne a dakatar da saida musu kudaden.
Ya ce yanzu haka sun samu labarin cewa akwai kungiyoyi masu zaman kansu gami da cibiyoyin hada hadar kudade da suka zama shafaffu da mai wanda yan kasuwa ke basu kudi ko ta hakin kaka.