A ranar Talata, 17 ga watan Satumba ne aka yi jana’izar babban limamin garin Agaie na jihar Neja, Sheikh Ahmadu Ndanusa bayan rasuwarsa a ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust suka tabbatar.
Sheikh Sani Abdulkadir Zaria ne ya jagoranci sallar jana’izar a gaban manyan mutane da suka samu halartar jana’izar kamarsu Etsu Agaie, Alhaji Yusuf Nuhu, Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, Sarkin Lapai, Alhaji Umar Bago da kuma manyan limaman Bida, Lapai da Doko.
An haifi marigayin ne a zamanin Sarkin Agaie na shida, Etsu Abdullahi, wanda ya yi mulki daga shekarar 1926 zuwa 1935, haka nan ya yi karatu a gaban Malamai daga ciki da wajen jihar Neja, har zuwa Zariya. Daga cikin malamansa akwai Malam Shehu Babango da Sheikh Abdulkadir Zaria, haka zalika ya rasu yana da mata 1 da yara 17 da jikoki 106, daga cikin yaransa akwai wani babban Malami dake garin Zariya, Sheikh Danlami Muhammadu Sani.