Hukumar da ke kula da katin shaidar zama dan kasa (NIMC), a ranar Laraba, ta sanar da cewa masu lambar dan kasa NIN za su biya N15,000 kafin a canja masu ranar haihuwa a rumbun ajiye bayanansu na hukumar.
Kodinetan NIMC na lardi, Funmi Opesanmo, ta bayyana hakan a ranar Labara a ofishin hukumar da ke Alausa, jihar Lagos.
A cewar ta, mamallakan lambar NIN za su biya N5,000 domin sabunta katin dan kasarsu ko kuma yin sabo idan wancan ya bace, da kuma biyan N500 idan za a canja adireshin da ke jikin lambar dan kasar.
KARANTA WANNAN: Da duminsa: CJN ya rantsar da mukaddashin babban Jojin FCT Abuja
Ta ce akwai ayyuka da dama da hukumar ta ke gudanarwa, tana mai nuni da cewa yin rejistar lambar NIN kyauta ne, amma akwai kudaden da ake biya idan za a sabunta katin, canja ranar haihuwa ko kuma canja adireshi.
Opesanwo ta ce, “Domin canja ranar haihuwa a lambar NIN, dole mutum ya biya N15,000. Domin sabunta kati ko kuma yin sabo idan wani ya bace, mutum zai biya N5,000. Sannan idan mutum zai canja adireshi ko suna, zai biya N500. Don haka, wasu na zargin cewa ana tambayar su kudi idan sun je yin rejista, dukkanin wadannan ayyukan da za a biya kudi, ayyuka ne na musamman ba kamar yin rejista ba.”
Jami’ar hukumar ta NIMC ta yi nuni da cewa ana biyan kudin ne a asusun bai daya na gwamnatin tarayya. “Domin canjin ranar haihuwa, kudinsa N15,000 ne kuma ana biya a asusun TSA,” a cewar ta.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta hannun hukumar sadarwa ta kasa NCC ta umurci kamfanonin sadarwa da su kulle layukan wayoyin da aka gaza hada lambarsu da lambar NIN.
Gwamnatin tarayya ta ce ta ba kamfanonin sadarwar wa’adi zuwa 19 ga watan Janairu su kulle layukan da ba a sabunta bayansu da lambar NIN ba, yayin da masu layukan aka basu wa’adi zuwa ranar 9 ga watan Fabreru.
Sai dai tuni mutane suka fara korafin cewa kamfanonin sadarwa sun fara rufe rayukan wayoyinsu tun kafin karewar wa’adin da gwamnatin ta bayar.
A wani labarin, Alhaji Abdullahi Umar Maitaro, ƙani ga Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ya rasu, yana da shekaru 57 da haihuwa sakamakon hatsari da ya rutsa da shi.
Maitaro da wasu abokansa guda biyu sun mutu ne sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a ƙauyen Muduru da ke kan hanyar Katsina zuwa Daura a ranar Lahadi, yayin da sauran da suka samu raunuka ke karbar magani a asibiti.