Gwamnatin tarayya ta ware makudan kudade kimanin biliyan hudu da digo takwas inda ta baiwa hukumar NIA don bin diddigin masu yin WhatsApp da duk wata hanya ta tura sakonni da maganganu. Kamar yadda Jaridar Thecable ta wallafa a shafinta
Jaridar The cable dai cewa tayi, ta gano hakane a cikin bojet da aka turawa Yan majalisu don bita a kanshi.
A ranar Laraba ne Yan majalisun kasar nan suka amince da miliyan #982 a matsayin wani bangare na bojet din 2021. An ware makudan kudade kimanin biliyan 895 domin hidimar kasa.
KARANTA:- Ya Kamata ‘Yan Fim mu rinka Auren junan mu~ inji Zakiyya Ibrahim Abdullahi
Bojet din wannan shekarar zai mai da hakaline wajan rashin tsaro dake addabar kasar nan. Sannan kuma da magance cutar Covid-19.
Daga cikin abunda ke kunshe cikin bojet din, ta bangaren Yan sanda an ware biliyan 33.6 don yin wasu ayyuka, sannan miliyan 200 za ai amfani da ita wajan yin feshin makarantun su da wajejen horas da mutanensu.
An kuma warema Yan sanda miliyan 936 domin sayen kayayyaki, sannan miliyan 910 don albashinsu da kuma alawansi na su.
A fannin gidan Sojin Kasa kuma, an ware biliyan #1.6 domin wasu sabbin Sojoji 2,700. Sannan sojojin sun samu miliyan #675 a matsayin alawansi na su.
Sojojin sama kuma sun samu jimillan kudi bilyan 239, a inda aka ware miliyan 266 don sayan kananan makamai, sannan miliyan 1.5 don gyaran barak, sannan biliyan 84 don biyan kayan aikin tsaro.
A fannin Jami’an farin kaya watau (DSS) kuma an ware bilyan 17.5, domin sayen Motocida gyare-gyaren Makarantun su.
Ta bangaren hukumar dake kula da yaduwar cutar kanjamau, an ware bilyan 1.6 don cigaban ayyukan kawo lafiya.
A inda aka ware biliyan 20.6 don rarraba Magungunan cutar Covid-19 zuwa kowane Kauye. An sayo Magungunan akan bilyan 60.7.
Sannan an ware bilyan 6.7 don shuka itatuwa domin samun iska a fadin kasar.