Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya sake jaddada kudurinsa na kaurace wa siyasar bangaranci, ya kuma ci gaba da zama dattijon dan siyasa.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu shugabannin jam’iyyar PDP da suka kai masa ziyara a dakin karatu na shugaban kasa da ke Abeokuta.
Tawagar wacce shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu ya jagoranta, ta hada da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2019 da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi; Sule Lamido na Jihar Jigawa; Olusegun Mimiko, Liyel Imoke, Donald Duke da dai sauransu.
Tsohon shugaban kasar ya yaba da wannan ziyara inda ya ce duk wanda ke son shawararsa a kodayaushe zai kasance a bude domin tuntubar shi domin amfanin Najeriya.
Inda ya ce amma shi babu abunda zai sake mayar da shi cikin jam’iyya.