Rundunar tsaron ta Civil defence reshen jihar Kano, ta yi watsi da wata sanarwa da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ‘yan bindiga daga jihohin Zamfara da Katsina na komawa jihar Kano.
Rahoton da ake zargin na bogi ne ya bayyana cewa ‘yan bindigar da suka tsere daga farmakin jami’an tsaro, ana kyautata zaton sun kutsa cikin jihar Kano da wasu yankunan al’ummomi a kananan hukumomin Shanono, Gwarzo da Kabo.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSC Ibrahim Idris-Abdullahi, ya fitar a Kano ranar Litinin.
“A ranar 28 ga Oktoba, da misalin karfe 9:00 na safe, an ga wasu mutane a kan babura suna tafiya daga kauyen Danguzuri da ke karamar hukumar Makarfi a jihar Kaduna.
Sai dai ya ce rundunar tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro za su ci gaba da kara sanya ido domin kaucewa duk wani abin da ka iya zama barazana ga tsaron jihar.