Hukumar kula da ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta gaza kare zargin da ake mata, kan zargin almundahana da dukiyar gwamnati da kuka ta al’ummar jihar wajen rufda ciki akan kudin.
Idan zaku iya tunawa lokacin afkuwar lamarin Jaridar Dimokuraɗiyya ta tuntubi Mai magana da yawun hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Naisa, karin haske kan karar shugaban hukumar da wasu ma’aikatan hukumar suka kai shugaban ta hukumar yaki da aikata rashawa ta ICPC, yayi alƙawarin binciken lamarin tare da bayar da amsa kan batun a ranar Litinin.
A yau wakilin Jaridar Dimokuraɗiyya a jihar Kano Ibrahim Hassan Hausawa ya tuntubi Nabulisi Kofar Na’isa domin jin a inda aka kwana.
A martanin da yake mayarwa da Wakilinmu bayan tambayarsa inda aka kwana, ya bayyana cewa bashi da wata taƙamaimai amsa da zai iya bayarwa kan wannan batu.
Hakan ya sa Jaridar Dimokuraɗiyya ta tambaye shi ke nan gaskiya ne zargin?
Ya bayar da amsar cewa baza iya cewa Eh ko A’a ba, saboda wadanda suka kai korafin sun kasa gano su a cikin ma’aikatan su, sannan adireshi da lambar wayar da suka yi amfani da da su dukkan su wasu na daban ne na hukumar.
A karshe dai yace bashi da wata ta cewa kan wannan batu.