Sufeto-Janar na Ƴan Sandan Najeriya IGP Usman Alƙali Baba yace babu wata ƴar sanda mace da za’a kora daga barikin ƴan sanda a faɗin ƙasar sabudda tana zaune da wani farar hula a tare.
Mai Magana da Yawun Rundunar na Ƙasa CP Frank Mba ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kano Za ta Zamanantar Da Kasuwannin Shanu 5 a Jihar
Yace Sufeto-Janar ya bada tabbacin hakan a lokacin da yake maida jawabi akan wata magana data fito daga Rundunar Ƴan Sanda ta Jahar Enugu dake cewa duk wata mace ƴar sanda dake zaune a barikin ƴan sanda dake zaune da mijinta farar hula su fita tare da mijin nata kafin 31 ga watan Janairun shekarar 2022.
Yace IGP ya bada umarnin gudanar da bincike akan al’amarin daya taso domin tabbatar dacewa anyi hukunci ga dukkanin wani mutum da aka samu da aikata laifin.
Acewar sa, Sufeto-Janar wanda ya kasance a halin na rashin jindaɗi akan dokar, ya bayyana ta a matsayin karya doka, da cin mutunci kuma ya saɓawa kundin tsarin aiki.
Yace dokar ta saɓawa raba dai-dai na jinsi na Rundunar Ƴan Sanda