Hukumar bunkasa noma da makiyaya ta jihar Kano (KSADP) ta ce za ta gyara tare da inganta kasuwannin shanu guda biyar a fadin jihar.
Daya daga cikin kasuwannin harda Kasuwar Shanu ta Falgore da ke Karamar Hukumar Doguwa.
A cewar kwararre kan harkokin sadarwa a kasuwannin, Ameen K. Yassar, kasuwannin za su kasance da wuraren lodi da saukar da Dabbobi, wuraren shayarwa, magudanun ruwa, ofisoshin Gudanarwa na kasuwa, tsaro da kiwon lafiyar dabbobi, fitulun kasuwanci da daddare da kuma bandakuna.
Ko’odinetan aikin Malam Ibrahim Garba Muhammad ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin wakilan kungiyoyin kiwo da noma na al’ummar Falgore, wadanda suka ziyarce shi a ofishin aikin.
Ya ce aikin ya kammala shirin samar da akalla cibiyoyin tattara madarar nono guda biyar a Falgore, inda ya bukaci jama’a da su goyi bayan manufofin.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar tare da hukumar KSADP na hada kai don ganin yadda za su bullo da wani shiri na bunkasa zamantakewa da tattalin arziki ga matasan Fulani.
Tun da farko wakilan kungiyar kiwo da noma, Malam Haruna Mu’azu da Ardo Umar Lawan Motar Kara sun bukaci KSADP da ta samar wa ‘ya’yansu makarantu, su sa jama’ar su cikin shirin na kiwo da kuma gina cibiyoyin tattara madara a cikin yankunan su.