Diyar dan majalisar dokokin Najeriya, Rabiyya Nasir Ahmad, ta karya tarihin jami’ar Landan, inda ta zama mace ta farko da ta kammala digiri a fannin shari’a da sakamakon ta daya Wato (first class).
Dimokuradiyya ta rawaito cewa Rabiyya Nasir Ahmad wadda Jami’ar Coventry ta Landan ta karramata digirin digirgir a fannin shari’a, ita ce bakar fata mace ta farko da ta yi irin wannan rawar a tarihin jami’ar, wadda aka kafa a shekarar 1992.
Mahaifinta, Nasir Ali Ahmad, dan majalisa mai wakiltar mazabar Nasarawa ta tarayya daga Kano wanda ke cike da farin ciki a ranar Alhamis, ya gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya baiwa ‘yar tasa matsayi wacce ta dage kan karatun lauya.
“Na amince da rokon da ta yi akai-akai na a bar ta ta yi karatun lauya, ba tare da sanin baiwar da Allah Ya yi mata ba,” in ji Ahmad mai cike da farin ciki.
”Gaskiya nasarar da ta samu ya kuma tabbatar da boyayyun hazaka da aka baiwa matasan Najeriya da dama”.
Comments 1