Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace Najeriya na fuskantar gagarumar matsaloli da ta shafi Noma wa da sarrafawa gami da safarar nau’ikan miyagun ƙwayoyi daban-daban a Ƙasar.
Ya bayyana hakan ne a Abuja a sakonsa na bude babban shirin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa mai shafuka 48, na shekarar 2021 zuwa 2025, wanda hukumar yaki da sha da hana fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta shirya a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-dumi: ‘Yan Sanda Sun Kama Daliban Kwalejin Dowen 3 Kan Mutuwar Oromoni
Ya ƙara dacewa, bincike da Hukumar kula da da Amfani da magani ta Ƙasa tayi, ya bayyana yawaitar amfani da magunguna ba bisa ƙa’ida ba a Ƙasar nan.
A cewar sa, idan ba’a magance wannan matsalar ba, zata kawo tsaiko ta fuskar lafiyar al’umma, ilmi, da rayuwar Al’umma , da tsaro da Hukuncin doka gami da kyakkyawan Shugaban ci.
Shugaban Ƙasar ya yi kira ga iyaye, da Malamai, da Ƙungiyoyi, dasu sanya dabi’ar yaƙi da miyagun Ƙwayoyi, musamman ga Matasa da Marasa galihu a cikin al’umma.
Comments 1