Bamu Shirya Karbar Yan Gudun Hijira Miliyan 240 Idan Najeriya Ta Wargaje
Vanguard ta wallafa cewar Majalisar Dinkin duniya ta gargadi matasan Najeriya dasu rinka bin doka da oda don gina kasar su, don a halin yanzu duniya bazata iya karbar Yan gudun hijira miliyan 240 daga Najeriya ba idan ta wargaje.
KARANTA:-Matashin da ya ce shi mala’ika ne, ya koma mutum bayan ganawa da Dakarun Hisba
Amina Muhammad ta bayyana hakan a wani jawabi da hukumar watsa labarai tayi tace Yan Najeriya dasuyi amfani da baiwar da Allah ya basu don gina kasar.
Ta kuma yi bayana kan koma baya da matasa suka kawo a lokacin zanga zangar #ENDSAR wanda abun ya koma a rushe kayan gwamnati da kone kone, sannan ta haddasa matsala ga kafafen sada zumunta.
Ta cigaba da cewa Matasa kuyi alfahari da Kasar ku Najeriya, kada ku rusata ku shirya, Kuna da Ilimi, Kuna da kayan aiki Kuma Kuna da babbar dama a nan gaba, amma tun kamin ku fara tafiyar kun fara aibata kan ku.
Kudaina hakan, kuyi matukar alfahari da Kasar ku Najeriya, ku daina rusata sannan kada ku gaza wajan gina ta.
Tun da Kuna ganin Najeriya na cikin runtsi, kuyi tunanin yadda zaku farfado da ita, idan kuka barta to ina zakuje?
Ina mai tabbatar muku a hanlin yanzu duniya bata da inda zata aje Yan gudun hijira miliyan 240 daga Najeriya, don haka mutsaya mu hada kanmu don ceto kasarmu Najeriya, mu gudu tare mu tsira tare.
Ta cigaba da cewa da akwai damammaki da yawa a kasar nan wanda ba’a fara anfani dasu ba.
Sannan matasan Najeriya su daina kwatanta kasarsu da wata.