A makon da ya gabata ne labarin wani matashi a jihar Bauchi ya bazama gari inda yake ikirarin cewa shi mala’ika ne.
Da ma dai wannan matashi mai suna Musa ya ce yan uwansa Mala’iku ne suka ruwaito mishi cewa shi ma mala’ika ne, amma kuma sun gaza bashi dama zuwa sama don a daura mishi ɗamara.
Cikin tattaunawarsa ta farko da Jaridar Dimokuradiyya, Musa wanda dan asalin Jihar Yobe ne amma yana leburanci a birnin tarayya Abuja, ya ce nan birnin tarayya Abuja ya gamu da yn uwansa Mala’iku suka raɗa mishi wannan mu’ujiza tasa.
Kuma bayan bayyanar wannan mu’ujiza ne dai matashi Musa ya bukaci a haɗa shi da manyan malamai don tabbatar masa da ita.
To sai dai bayan ganawarsa da dakarun Hisba a karshen mako a Bauchi, Musa Karkum ya gane cewa lallai fa shi mutum ne ba mala’ika ba, a baya ma da ya ce mala’ika ne shi shafar aljanu ne.
Daga bisani ya bukaci manyan malamai da su taimaka su cire masa wadannan aljanu don shafa wa kansa lafiya.
Comments 1