Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Hon. Lucky Aiyedatiwa, a ranar juma’a ya bayyana cewa bai yi murabus daga mukaminsa na zababben mataimakin gwamnan jihar ba, yana mai cewa, “Na ci gaba da zama a matsayin mataimakin gwamnan jihar Ondo.” Tribune Online ta rawaito.
Ayedatiwa, wanda ya ke mayar da martani kan wasu kafafen yada labarai na yanar gizo cewa ya yi murabus daga mukaminsa na mataimakin gwamnan jihar a wata takarda da ya rubuta kafin ya rattaba hannu, ya ce ba shi da niyyar yin murabus, yana mai bayyana rahoton a matsayin hasashe na marubucin.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabon Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN
A wata sanarwa da Ayedatiwa da kansa ya sanyawa hannu kuma aka bai wa manema labarai a jihar, mataimakin gwamnan ya musanta labarin da cewa an shirya shi ne domin kawo rashin jituwa a jihar.
Mataimakin gwamnan na Ondo ya gargadi masu yada labaran da su kaurace wa irin wannan aika-aikar, inda ya bukaci al’ummar jihar da su yi watsi da batun murabus din.
Wasikar ta ce: “An ya ja hankali na ga jita-jitar da ake yadawa cewa takardar murabus din da na sa hannu a kai, da ake yadawa a bainar jama’a.
“Ina so in bayyana cewa ni Lucky Orimisan Aiyedatiwa, Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo, ban yi niyya ba, kuma ba zan sanya hannu a wata takarda ta ajiye mukamina na Mataimakin Gwamna da aka zaba a tikitin hadin gwiwa da Gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Odunayo Akeredolu ba.
Ya ce, “Na yi rantsuwa a ranar da aka rantsar da ni tare da Gwamna a ranar 24 ga watan Fabrairun shekarar 2021, don kare kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya a kan wa’adin shekaru hudu da zai kare a ranar 23 ga watan Fabrairu, 2025.
“Na kasance da aminci ga Shugabana, kuma na tsaya kan rantsuwar da na yi da Littafi Mai Tsarki na gudanar da cikakken zagayowar shekaru hudu tare da Gwamnan Akeredolu.
“Don haka, ina kira ga al’ummar jihar Ondo, majalisar dokokin jihar, da sauran jama’a da su yi watsi da irin wannan wasika a yanzu da kuma nan gaba.”
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Zai Bar Abuja Zuwa Wani Muhimmin Taro a Kasar Waje
Shugaba Bola Tinubu a ranar Lahadi ne zai bar Abuja, domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) 2023, wanda za a gudanar a birnin New York na kasar Amurka.
Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Ajuri Ngelale,shi ne wanda ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a.
Ya ce shugaban, baya ga babban taron majalisar dinkin duniya, zai gana da manyan masu ruwa da tsaki a harkokin tattalin arziki a duniya.
“Baya ga alkawurran da zai yi a zauren Majalisar, baya ga aikin shigar da tawagar Najeriya a Majalisar, akwai wasu ayyuka masu matukar muhimmanci da za su yi tasiri a kan tattalin arzikin Najeriya.