Gwamnatin Adamawa za ta sake gina gadar sama da Sabon Rumbun ajiye Abinci a Yola
Majalisar zartaswar Jihar Adamawa a ranar Juma’a ta amince da sake gina wata gadar sama a Yola babban birnin Jihar dai-dai shatale-talen Mubi.
Wannan zai zama gadar sama ta uku a Yola bayan aka kammala guda biyu a shekarar 2021 da 2022 a wa’adin farko na Gwamna Ahmadu Fintiri.
Ana sa ran sabuwar gadar saman zata laƙume ma Gwamnatin Jihar kusan Naira biliyan 9.2.
Taron na Majalissar zartaswar Jihar a ranar Juma’a wanda Fintiri ya Jagoranta, ya kuma amince da gina sabuwar babbar hanya mai tsawon kilomita 20.8 wadda ta fara daga wani wuri mai suna Barka da zuwa Yola wato bakin shigowa gari, ta bi ta hanyar barikin sojoji, inda ita kuma za ta lashe kimanin Naira biliyan 21.8.
KARANTA NAN:Muna da yaƙini akan Dattakun Kwankwaso – shugabannin NNPP na Kudu maso Yamma
Kwamishiniyar yaɗa labarai da tsare-tsare ta Jihar Adamawa Mrs Neido Geoffrey Kofulto ta shaidawa manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron a gidan Gwamnatin Yola cewa gadar saman za a kammala ta cikin watanni 18, yayin da babbar hanyar za a kammala ta cikin watanni 30.
“Idan aka kammala ayyukan za su rage cunkoson ababen hawa da kuma ƙara kyautata ayyukan zamantakewar al’umma a Jihar,” inji ta
Kofulto ta kuma bayyana cewa Majalisar ta amince da gina wani rumbun ajiye abinci a gidan Gwamnatinti Yola domin hana ɓata gari afkawa gami da wawushe abincin Jihar kamar yadda su kayi a kwanakin baya.
Ta ce rumbun ajiyar wanda ke girman ɗauke Tan 7800 na shinkafa da sauran hatsi an bayar da kwangilar gina shi ne ga Medugu Commercial and Construction Company akan kudi Naira Miliyan 291.
A wani labarin kuma:Ministan Abuja ya baiwa Masu Sarautar Gargajiya 10 Kyautar Sabbin Motoci
Ministan Abuja ya baiwa Masu Sarautar Gargajiya 10 Kyautar Sabbin Motoci
Ministan babban Birnin Tarayya (FCT) Nyesom Wike ya baiwa wasu masu Sarautar Gargajiya 10 kyautar Motoci babban birnin Tarayya Abuja a ranar Juma’a, tare da alkawarin inganta rayuwar sarakunan gargajiya.
Kamfanin dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa sarakunan sun fito ne daga Masarautar Gomani, da Yaba, da Bwari, da Pai, da Garki, da Jiwa, da Wako, da Rubochi, da Gwagwalada da kuma Zuba duk a Abuja.